Ana kara matsawa Shugaban Masar lamba

Masar Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu zanga-zanga na ci gaba da nuna kin jinin shugaba Mubarak

Har yanzu shugaba Hosni Mubarak naci gaba da fuskantar matsin lamba kan ya sauka daga mulki nan take, bayan da ya bayyana cewa ba zai sake tsayawa takara ba.

Shugaba Barack Obama na Amurka ya ce lallaine a fara sauyi cikin kwanciyar hankali "nan take", yayin da Fira Minstan Turkiyya Erdogan ya ce ya kamata Mr Mubarak "ya dauki wata hanyar daban".

A jawabin da ya yi ga jama'ar kasar ranar Talata, Mr Mubarak ya yi alkawarin ba zai kara tsayawa takara ba, sannan ya sha alwashin kawo sauye-sauye kan tsarin mulkin kasar.

Dubban jama'a ne suka fita kan tituna domin nuna goyan bayan a gare shi ranar Laraba.

Sun ce suna magana ne da yawun ainahin jama'ar Masar, ba biyansu aka yi domin su yi zanga-zanga ba, a cewar wakiliyar BBC Jon Leyne a birnin Alkahira.

Yayin da ragowar, wadanda ke kusa dandalin Tahrir, ke cewa alkawarin nasa bai wadatar ba: "Ba za mu bar nan ba! Dole ne ya sauka!"

Rundunar sojin kasar - wacce ake kallon 'yar baruwa na a rikicin - ta bada sanarwa, inda ta yi kira ga masu zanga-zangar da su koma gidajensu, domin al'amura su koma daidai a kasar.

"An saurari sakonnin ku, bukatarku ta fito fili..... Za ku iya mayar da al'amura yadda suke," Kamar yadda mai magana da yawun sojin ya fada a gidan talabijin din kasar.

A bangare guda kuma, hanyoyin sadarwa na intanet da wayar salula sun fara koma wa daidai bayan da gwamnati ta katse su na wasu kwanaki.

Karin bayani