Hukumar zaben Nijar Ceni ta kusa bayyana sakamako

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

A Jamhuriyar Nijar ya rage saura 'yan sa'oi kadan a bayyana sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki.

Shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta CENI, ya bayyanawa manema labarai cewa hukumar za ta fadi sakamakon zaben idan an jima.

Cikin 'yan takara da suka baiwa abokan adawar su rata a zaben sun hada da Shugaban Jam'iyyar PNDS Tarayya, Mahamadou Issoufou da Shugaban Jam'iyyar MNSD Nasara Malam Seini Oumarou.

A rananr Litinin din da ta gabata ne dai aka jefa kuri'a domin zaben shugaban kasa da 'yan majalisar dokokin jamhuriyar Nijar.