Torres zai fara taka leda a wasan Chelsea da Liverpool

Fernando Torres
Image caption Fernando Torres ya koma Chelsea a matsayin dan wasan da ya fi kowanne tsada a Burtaniya

Kocin Chelsea Carlo Ancelotti ya ce mai yiwuwa dan wasan da ya fi kowanne tsada a Burtaniya Fernando Torres, ya fara taka leda a wasan da Chelsea za ta yi da Liverpool ranar Lahadi.

Dan wasan na Spain tare da na Brazil David Luiz, doka ta hana su taka leda a wasan da Chelsea ta casa Sunderland da ci 4-2.

"Za mu gwada shi gobe da kuma jibi. Idan ba shi da matsala, zai fara buga wasa," a cewar Ancelotti.

"Amma ba shi da wata matsala tun da ya buga wasan karshe da Liverpool ta yi".

Ancelotti ya kuma ce babu wata damuwa zai iya hada Torres da daya daga cikin Nicolas Anelka, wanda ya zira kwallo a wasan su da Sunderland, da kuma Didier Drogba.