Bamu da hannu a rikicin Alqahira- Pira Minista

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ahmad Shafiq

Sabon Fira ministan kasar Masar Ahmad Shafiq ya bayar da hakuri game da batakashin da aka yi a tsakiyar birnin Alqahira, sannan yayi alkawarin gudanar da bincike.

Sai dai yayi watsi da zargin da ke cewa gwamnati na da hannu wajen kawo magoya bayan shugaba Hosni Mubarak wadanda suka kai harin kan masu zanga-zangar kin nuna jinin gwamnati.

Za'a iya cewa tarzoma da ake ci gaba da ake yi a masar ta kawo rarabuwar kawuna da kuma rudani tsakanin jamian gwamntin kasar.

Haren haren da aka kaiwa masu gunadra da zangar zanga cikin lumuna a dandalin tahrir, jama'a da dama sun yi ammana cewa 'yayan jamiyar kasar me mulki ce suka shirya su.

Wani me rike da babban mukami a jamiyyar ya zargi wasu abokane aikinsa da shirya tashen tashen hankula. Sai dai Gwamnatin kasar ta ce bata taka wata rawar ba tashen tashen hankulan.

Fri ministan Masar Ahmed Shafiq ya nemi afuwa a jawabin da ya gabatar a gidan talibijin na gwamnatin kasar kan tarzomar da ta barke a tsakiyar birnin Alqahira a jiya.

Mr Shafiq ya sha alwashin gudanar da bincike kuma ya ce za'a hukunta duk wani wanda aka kama da hanu cikin tashen tashen hankula.

Sai dai da aka nemi ra'ayinsa akan ko ya amince shugaba Mubrak ya sauka daga kan karagar mulki yanzu sai ya ce ; "Shin ko wanan shine lokacin da ya kamata ace ya sauka? bana tunanin haka saboda muna da wani gungun ministocci da zasu tsara abubuwan da za'a gudanar a kasar da jama'ar za su amince da su."

Bugu da kari Sakatare janarar na majalisar dinkin duniya Banki Moon ya shaidawa BBC cewa ba za su amince da tashe tashen hankula da suka faru a ranar laraba ba; "Na damu matuka kan tarzomar da ake cigaba da gudanarwa. Ina ta kira ga dukannin bagarorin akan bukatar ganin cewa sun yi hakuri, kuma ya kamata hukumomi kasar su tabatar cewa ba a kaiwa masu gudunar da zanga zanga cikin lumuna hari ba."

Yanzu dai fargabar da ke ita ce rarabuwar kawunan dake tsaaknin jamian gwamnati abun da kuma watakila ya jinkirta duk wani matakin gaggawa da za'a dauka domin kawo karshen wanan rikici