Facebook: 'Shari'a ce za ta raba mu da Sule Lamido'

A Najeriya, iyalan matashin nan Moukhtar Ibrahim Aminu, da aka kama a jihar Jigawa sanadiyyar kakkausar addu'ar da ya yi wa gwamna Sule Lamido a shafinsa na Facebook sun ce za su shigar da kara bisa keta masa hakkin bil adama da suke zargin gwamnan ya yi.

Matashin, wand aka kwantar a asibiti bayanda kotu ta sallami kararsa da aka shigar ya shafe kwanaki goma a gidan kaso, abinda iyalan nasa ke cewa shi ya haddasa masa rashin lafiya.

Tuni dai wata kungiyar 'yan Najeriya mazauna Burtaniya mai fafutukar tabbatar da dimokradiyya, mai suna Nigeria Liberty Forum ta kaddamar da wani gangami na intanet na Allawadai da abinda ta kira danne hakkin fadin albarkacin baki da gwamnan jihar Jigawan ke kokarin yi.

Gwamnatin jihar Jigawa dai ta janye karar da ta kai matashin Moukhtar Ibrahim Aminu ne, bayan ta zarge shi da wallafa kalaman batunci ga gwamna Sule Lamido a shafinsa na facebook.

Kakkausar addu'a

Shi dai matashin ya rubuta wata kakkausar addu'a ne da ya nemi narkon ubangiji kan gwamna Lamido da abokanansa.

Kan haka ne aka kama shi tare da mika shi ga hedkwatar hukumar 'yan sandan Najeriya da ke Abuja, inda bayan kwanaki tara a tsare, hedkwatar 'yan sandan ta mayar da shi jihar Jigawa.

Image caption Gwamna Sule Lamido na Jihar Jigawa a Najeriya

A nan aka gurfanar da shi gaban kotun majistare ta mai shari'a Mustapha Sa'ad, wanda ya tura shi karin zaman kaso na mako guda a gidan wakafi.

Sai dai kuma bayan kwana guda sai aka sake shi bayanda aka ce gwamnatin ta janye karar.

Mahaifin Matashin Ibrahim Aminu ya shaidawa BBC cewa matashin yana asibiti yana samun kulawa sanadiyar tsarewar da aka yi masa; " Ina son jin ta bakin likitoci tukunna kan lafiyarsa, kafin in daukaka kara, saboda an keta hakkinsa a matsayin dan adam."

'Kullin siyasa ne'

Mahaifin yaron wanda dan siyasa ne ya ce, matakin da gwamnatin Sule Lamido ta dauka kan dan sa, bita da kullin siyasa ne, saboda ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP ta gwamnan zuwa jam'iyyar adawa ta ACN.

Sai dai gwamnatin jihar Jigawan ta musanta wannan zargi, kamar yadda kakakinta Umar Kyari Jitau Madamuwa ya ce babu hanun gwamnan a tsare matashin; " Jami'an tsaro ne kawai su ka ga matsahin ya keta dokar kasa kuma suka tsare shi."

"Kuma jami'an tsaron ne da kansu su ka janye karar." In ji Umar Kyari.

Tuni dai wata kungiyar 'yan Najeriya mazauna Burtaniya mai rajin kare hakkin dimokradiyya Nigeria Liberty Forum ta kaddamar da wani gangami na yin tur da gwamna Sule Lamido a shafinsa na Facebook.

Wannan kira dai ya haddasa sa-in-sa a shafin facebook na gwamnan mai abokan mu'amala sama da dari bakwai, inda wasu ke yi masa tofin alatsine yayinda wasu ke ganin cewa Moukhtar ya nuna rashin tarbiyya a cikin wannan addu'a da ya wallafa.

'Halattattun bukatu ne'

Shugaban kungiyar Nigeria Liberty Forum, Mr. Kayode Ogundamisi ya ce:

"Muna kakkausar suka ga yunkurin gwamna Sule Lamido na murkushe muryar 'yan adawa. Muna ganin rashin adalci a Jigawa, daidai ne da rashin adalci ga kowa a Najeriya, kuma aikinmu ne mu sanar da kasashen duniya halin da ake ciki."

To ko Mr. Ogundamisi baya ganin addu'ar da Mukhtar ya wallafa a facebook ta wuce makadi da rawa?

Ya ce; "Babu wani waje a cikin addu'ar da matashin ya yi kira ga mutane da su kashe gwamna Lamido ko kuma su kai masa hari."

"Kawai dai ya roki Allah ne ya tarwatsa Sule Lamido da abokan Lamido da ka iya taka rawa wurin talauta matasa a arewacin Najeriya, ko kuma suka sai da mutuncinsu don samun abin duniya." In ji Kayode.

Kayode ya kuma kara da cewa: "Wadannan halattattun bukatu ne kuma in har Najeriya tana son aiwatar da tsarin dimokradiyya, to batun ya zarta kawai ikon yin zabe ko tsayawa a zabeka, abin ya hada da hakkin mutane su bayyana albarkacin bakinsu, matukar dai ba su keta hurumin shari'a ba."

Wannan badakalar dai na faruwa ne daidai lokacin da zabubbukan gama-gari ke kara kusatowa a Najeriyar, inda doka ta halatta fadin albarkacin baki amma mahukunta kan hana yada labaran