Ba tantama za'a je zagaye na biyu a zaben Nijar

Hakkin mallakar hoto AFP

A Jamhuriyar Nijar ana sa ran sakamakon zabbukan 'yan majalisar dokoki na kasa da na shugaban kasa da aka gudanar a farkon mako.

Hukumar zabe mai zaman kanta CENI ta ce za ta bayyana sakamakon ne a yau.

Daga kuri'un da aka kirga alamu na nuni da cewa a cikin 'yan takarar shugaban kasa mutum goma, mutum biyu ne a sahun gaba wato Shugaban Jamiyyar PNDS Tarayya Alhaji Mahamadou Issoufou da dan takarar Jamiyyar MNSD Nasara Alhaji Seini Oumarou.

Sai dai shugaban hukumar zaben kasar Mai Shara'a Gousmane Abdurahamane ya ce, babu makawa sai an je zagaye na biyu na zaben a wata mai zuwa, domin babu wani dan takarar da ya samu nassararar kashi 50 cikin dari.