Yau wa'adin rajistar zabe a Najeriya ke cika

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

A yayinda karin wa'adin rajistar masu zabe ke cika a yau a Najeriya, wasu 'yan kasar na kira ga hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC da ta kara wasu kwanakin domin baiwa duk wadanda suka cancanci kada kuri'a damar yin rajistar.

Duk da karin na'urorin da Hukumar ta kara domin tabbatar da kowa ya yi rajistar, mutane da dama na korafin rashin yin rajistar, ko kuma shafe tsawon lokaci a layuka.

Hukumar INEC a baya ta kara mako guda akan wa'adin makonni biyu da ta ware da fari domin yin rajistar zabe, duk da cewa sauyin da aka yiwa dokar zaben kasar ya bata damar karin wata guda.

Sai dai hukumar na cewa ta na cigaba da daukar matakan tabbatar da kammala rajistar kafin yammacin yau.