Sakamakon zabe a Nijar ya yi wa wasu dadi

Hakkin mallakar hoto AFP

A Jamhuriyar Nijar wasu Jam'iyun siyasa sun soma bayyana farin cikinsu dangane da kyakkyawar sakamakon da suka samu a zaben 'yan majalisar dokoki da na shugaban kasa zagaye na farko.

Hukumar zabe ta kasa CENI ta bayyana cewa rashin samun nasarar kashi hamsin cikin dari daga bangaren wani daga cikin 'yan takarar shugabancin kasar a zaben da aka yi a ranar 31 ga watan Janairun da ya gabata, ya sa za'a je zagaye na biyu.

Jam'iyun musamman ma na kan gaba sun bayyana kyautata zaton lashe zaben da za'a sake fafatawa a zagaye na biyu, wanda za'a yi ranar 12 ga watan Maris mai zuwa.

A jiya ne dai hukumar zaben kasar CENI ta bayyana sakamakon zaben wanda ya tabbatar da Jam'iyar PNDS Tarayya ce ke kan gaba, sannan sai Jam'iyar MNSD Nasara ta tsohon shugaban kasa Tanja Mamadu.