Burtaniya ta gaza cimma al'adu barkatai

Praministan Burtaniya Hakkin mallakar hoto PA
Image caption David Cameron

Praministan Burtaniya David Cameron ya ce yunkurin da aka yi na mayar da kasar mai rungumar al'adu barkatai ya gaza, don haka ya kamata a maye gurbin hakan da cusa ra'ayin kishin kasa, wanda kowa zai iya runguma.

Cikin wani jawabi da ya gabatar, a wani taron harkokin tsaro a Jamus, Mr. Cameron ya ce kasashen Turai sun dade suna fargabar tunkarar matsalar cusa tsattsauran ra'ayin Islama a tsakanin musulmi.

Ya ce, "tilas ne mu haramta wa masu cusa akidar kiyayya zuwa kasashenmu. Wajibi ne kuma mu rusa kungiyoyin dake tunzurawa ana kai hare haren ta'addanci a kan mutane, a gida da waje."

Ya kuma ce akwai bambanci tsakanin masu tsattsauran ra'ayi, da sauran Musulmi mafiya rinjaye.