An soke ziyarar Bush zuwa Switzerland

George W Bush
Image caption Tshohon shugaban Amurka

An soke wata ziyara da aka shirya tsohon shugaban Amurka, George W Bush za kai kasar Switzerland, sakamakon tarzoma da kiran da ake yi na a kama shi.

Wata kungiyar Yahudawa wadda ta gayyace shi zuwa bikin a Geneva ta ce ta soke gayyatar, saboda hadarin jerin zanga zanga.

A wannan makon ne kungiyar yaki da azabtarwa ta duniya ta yi kira ga hukumomin Switzerland da su kaddamar da bincike, da nufin tuhumar Mr Bush kan zargin ya bada umurnin a ganawa wasu azaba.

Mr. Bush din dai ya amsa cewa ya bada umarnin amfani da abinda ya kira tsauraran dabarun bincike da ya ce ba su sabawa doka ba.