Masar ta dakatar da fitar da iskar gas

Tutar Masar
Image caption Tutar Masar

Masar ta dakatar da tura iskar gas zuwa Isra'ila da Jordan da kuma Syria, bayan fashewar wani bututu a yankin arewacin Sinai, kusa da kan iyaka da Isra'ila.

Fashewar bututun gas din, ya haddasa tashin gobara, wadda ake iya tsinkaya daga nisan kilomitoci masu yawa.

A yanzu an shawo kan wutar sai dai har yanzu ba a tantance dalilin da ya sa bututun yin bindiga ba.

Kodayake akwai rahotannin dake cewa mai yuwa yunkuri ne na yin zagon kasa.

Isra'ila na smaun kashi arba'in cikin dari na iskar gas din ta ne daga kasar ta Masar.