Tattaunawa da 'yan adawa a Masar

Omar Suleiman na Masar Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mataimakin shugaban kasar Masar

Ministan kudi a sabuwar gwamnatin Masar da shugaba Hosni Mubarak ya kafa ya shaidawa BBC cewa mataimakin shugaban kasa, Omar Suleiman na dab da fara wata tattaunawa da wasu shugabannin 'yan adawa.

Tun da farko kungiyar 'yan adawa mafi girma, ta 'Yan Uwa Musulmi ta fitar da sanarwar dake cewa a shirye take ta tattauna da gwamnati, amma ta ce wajibi ne shugaba Mubarak ya sauka daga mulki.

Daya daga cikin shugabannin, Muhammad Bishir ya ce, "dukkan mutanen dake bisa tituna a yanzu, a birane, da daukacin al'umar kasar Masar na adawa da shi, suna son ya yi murabus."

A wani taro a Jamus, sakatariyar wajen Amurka, Hillary Clinton ta ce yankin Gabas ta tsakiya na fuskantar wata guguwar sauyi ta neman kafa dimokradiyya.

Yanzu haka dai, masu zanga zanga na ci gaba da mamaye dandalin Tahrir a tsakiyar birnin alkahira, bayan gagarumar zanga zangar da suka gudanar jiya Juma'a ta nuna kyamar gwamnati.

Al'amura dai sun lafa, yayinda sojoji ke sa ido kan shiga da fitar dandalin, suna kuma duba katin shaidar jama'a.

A gobe ne kuma ake sa ran za a fara bude bankuna a kasar ta Masar.

Sai dai ita kasuwar hadahadar hannayen jari ta Alkahira ba zata bude bai sai jibi Litinin, kamar yadda aka bada sanarwa tun farko.