'Yan adawar Gombe na zargin gwamnati da muzgunawa

A Najeriya, 'yan adawa a Jihar Gombe na zargin gwamnatin Jihar karkashin Jam'iyyar PDP da muzguna masu musamman a yanzu da ake tunkarar zabuka a kasar.

'Yan adawar dai na cewa ana amfani da Jami'an tsaro da matasa 'yan-bangar siyasa da aka fi sani da suna 'yan kalare, domin hana su sakat a Jihar.

Ko a 'yan kwanakin nan, rahotanni sun bayyana cewa Jami'an tsaro sun kai samame a gida da kuma ofishin dan takarar Gwamnan Jihar karkashin inuwar Jam'iyyar adawa ta ANPP, inda suka yi amfani da barkonon tsohuwa tare da yin awon gaba da wasu magoya bayan dan takarar.

Ita dai Jam'iyyar PDP mai mulkin Jihar ta musanta wannan zargi, inda su kuma Jami'an tsaro suka bayyana cewa aikin nasu na tafiya ne daidai da dokar kasar.