Lika hotuna 'yan takara ya zama rigima a Kebbi

A Jihar Kebbi dake Najeriya, batun sakawa da cire hotunan 'yan takara ko allunan tallan 'yan takarar ya fara haifar da zaman tankiya a tsakanin magoya bayan gwamnati da 'yan adawa.

Wanann lamari dai ya fara haifar da tashin hankali a wasu sassan Jihar.

Yanzu haka dai Jam'iyyar adawa ta CPC a Jihar kebbi ta kira wani taron manema labarai inda ta zargi gwamnatin Jihar da kokarin hana ta tallata manufofi da kuma 'yan takarar ta, ta hanya ciccire allunnan tallan 'yan takarar jam'iyyar dake ko'ina a Jihar.

Sai dai gwamnatin Jihar ta musanta daukar mataki akan duk wani abu da wata Jam'iyyar ta yi a Jihar, in ba wanda ya sabawa kaida ba.