Gobara ta haddasa asarar rai da ta dukiya a Birnin Gwari

Wani hadarin tankar mai a Nijeriya
Image caption Wani hadarin tankar mai a Nijeriya

A Najeriya, hadarin motocin dakon mai ya jawo gobarar da ta haddasa asarar rai da dukiyoyi a garin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

Wani da abin ya faru kan idonsa ya ce ya ga gawa guda, kuma shaguna da dama dake bakin hanya sun kone kurmus..

Mahukunta jihar ta kaduna wadanda suka tabbatar da faruwar hadarin na cewa za su dauki kwararan matakai domin kawo karshen yawan hadarurrukan mota da ake fama da su a kasar.