Gwamnati da 'yan adawa na tattaunawa a Masar

Tattaunawa tsakanin gwamnati da 'yan adawa a Masar Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tattaunawa tsakanin gwamnati da 'yan adawa a Masar

Bayan kusan makonni biyu da aka kwashe ana zanga zangar nuna kyamar gwamnati a Masar, mataimakin shugaban kasar, Omar Suleiman ya fara tattaunawa da kungiyoyin 'yan adawa.

Daga cikin wadanda ake tattaunawa da su akwai Kungiyar 'Yan Uwa Musulmi, da wakilan matasan dake kan gaba wajen zanga zangar.

Essam el Erian, daya daga cikin shugabannin kungiyar ta 'yan Uwa Musulmi ya ce yanzu iko ba ya hannun shugaba Mubarak.

Ya kara da cewa a yanzu su na tattaunawa da mataimakin shugaban kasa domin duba tanajin da aka yi na dawo da zaman lafiya a kasa, da samar da tsaro da kuma tsarin dimokradiyya.

Kungiyar ta 'Yan Uwa Musulmi ta ce har yanzu tana kan bakarta sai shugaba Mubarak ya yi murabus, a kuma kafa gwamnatin rikon kwarya.