INEC ta ce za ta wallafa sunayen 'yan takara a mazabunsu

Shugaban Hukumar zabe, Parfesa Attahiru Jega
Image caption Shugaban Hukumar zabe, Parfesa Attahiru Jega

A Najeriya, yayin da a yau `yan kasar ke jiran jerin sunayen `yan takarar da jam`iyyun siyasa suka gabatar ma hukumar zabe, domin shiga babban zabe mai zuwa, Hukumar ta ce ta fito da wani sabon salon bayyana sunayen `yan takarar.

Sabanin yadda aka saba a baya inda take kafe sunayen a hedikwatarta da ke Abuja, hukumar ta ce yanzu ta tura sunayen ne zuwa mazabun da `yan takarar suka fito, domin jama`a su samu damar tantancewa da kansu.

`Yan kasar dai sun dade suna jiran ganin sunayen `yan takarar sakamakon takaddamar da ke tattare da yadda wasu daga cikinsu suka samu tikitin tsayawa takarar.