An fara sauraren shariar wasu Amirkawa a Iran

Amirkawan da ake zargi da leken asiri Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Amirkawan da ake zargi da leken asiri

Wata kotu a Iran ta fara sauraron wata shari'a a asirce, inda ake tuhumar wasu Amurkawa matasa su uku da leken asiri.

Alkalai a Tehran sun hana kafafen yada labarai halartar zaman farko na sauraron shari'ar.

Wakilin BBC ya ce, Amurkawan uku, Shane Bauer, da Josh Fattal da kuma Sarah Shourd, ana zarginsu ne da shiga kasar ba da izini ba, da kuma leken asiri, bayan da aka kama su a kan iyakar Irin din da Iraki, a 2009.

Amma sun ce suna yawon bude ido ne, suka yi kuskuren shiga Iran.

Ita dai Miss Shourd an bada belinta a bara, har ma ta koma gida Amurka, yayinda ake ci gaba da tsare sauran biyun a Iran.