An samu cikas a tattaunawar gwamnati da 'yan adawa a Masar

Masu zanga zanga a kasar Masar Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wasu jam'iyyun adawa a kasar Masar sunyi korafin cewar gwamnati bata kira su tattaunawar da take yi da 'yan adawa ba

Yayinda aka soma wata tattaunawa tsakanin gwamnati da wasu jam'iyyun adawa a kasar Masar, wasu jam'iyyun adawar kasar sun yi korafin cewar ba'a basu goron gayyata zuwa wannan tattaunawa ba.

Jam'iyyar Al Ghad na daga cikin irin wadannan jam'iyyu kuma babban sakatarenta Wael Nawara ya shaidawa BBC cewar ba a sanya su cikin tattaunawar ba.

Ya kara da cewar har yanzu gwamnatin kasar na zabar wadanda take son ta tattauna dasu, ba tare da tuntubar ainihin kungiyoyin daya kamata ace an tattauna da su ba.

Baya ga irin wadannan jam'iyu dake kukan ba a dama dasu ba, ga alamu har yanzu hatta su kansu masu zanga zangar basa cikin wani yanayi dake nuna alamun cewar zasu sauko daga kan matsayinsu

Masu zanga zangar har yanzu sun hakikance cewar sai dai shugaba Mubarak ya sauka nan take

Sun kuma nemi da a rusa majalisar dokokin kasar wacce suke yiwa kallon haramtaciyya. Sun kuma ce shugabannin adawar kasar wadanda ake tattaunawar da su, ba su suke wakilta ba .

Halin da ake ciki dai ko shakka babu dai zai kara dagula tattaunawar da shugabannin siyasar suke yi da mataimakin shugaban kasar Omar sulaiman, wajen lalubo hanyoyin da za'a kafa sabuwar gwamnati a kasar.