Dubban jama'a sun yi jerin gwano a Senegal

Masu zanga-zanga a lokacin taron da aka yi a Brazil a 2009
Image caption Masu zanga-zanga a lokacin taron da aka yi a Brazil a 2009

Dubban jama'a ne suka yi jerin gwano a Dakar, babban birnin kasar Senegal, yayinda ake bude babban taron kyautata zamantakewar al'umma,wanda ke adawa da Babban taron duniya kan habaka tattalin arziki da ake gudanarwa a Davos.

Wadanda suka shirya taron sun ce nahiyar Afrika babbar misali ce ta gazawar wasu manufofin da aka shafe shekaru talatin ana aiwatarwa.

Mahalarta taron suna kuma mayar da hankali kan irin tarzomar dake faruwa a Tunisia da Masar.

Wannan dai shi ne karon farko da wata kasar Afurka mai amfani da harshen Faransanci ke daukar bakuncin taron na shekara- shekara.