Wata jami'ar gwamnatin Algeria ta yi kiran kawo sauyi a kasar

Wata tarzoma a Algeria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jamaa sun yi tarzoma a Algeria a watan jiya

Wata kusa a jam'iyyar dake mulki a Algeria, ta soki gwamnatin kasar da babbar murya, tare da yin kira da a shigo da sabbin jini cikin tafiyar da harkokin mulkin kasar.

Zohra Drif Bitat, mataimakiyar shugaban majalisar dattawan kasar ta ce duk da irin makudan kudaden da kasar ke samu daga cinikin mai da iskar gas, har yanzu jama'a na fama da talauci.

Wakilin BBC ya ce furucin na ta ya nuna irin damuwar da shugabannin kasar ta Algeria ke nunawa ne don kada guguwar neman sauyin da ta kada a kasashen Tunisia da Masar ta afka musu.