Wutar daji ta rusa gidaje 59 a Australia

Wutar daji ta rusa gidaje 59 a Australia Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wannan ne bala'i na baya-bayan nan da ya afkawa Australia

Wutar daji wacce ke ci gaba da ruruwa ba kakkauta wa a Yankin Perth na Yammacin Australia, ta yi awan gaba da gidaje akalla 59.

Masu aikin kashe gobara na fadi-tashin kawo karshen wutar a Gabas da Arewacin birnin, inda aka bayyana yankin da cewa yana cikin mummunar matsala.

Tuni dai daruruwan mutane suka fice daga yankin.

Wannan wutar na zuwa ne shekaru biyu bayan da mutane 173 suka mutu a wutar dajin da ta mamaye jihar Victoria.

Fiye da ma'aikatan kashe gobara 100 ne ke ta kokarin kashe wutar ta kasa da kuma ta sama, wacce ke ta karuwa a yankin na Perth.

An bada rahotannin cewa karfin wutar ya kai mita uku, inda ta kona gidaje 59 sannan ta lalata kusan talatin.

Wani babban jami'in kula da ayyukan gaggawa Craig Hynes, ya ce kawo yanzu babu wani bayani na samun mummunan rauni.