Shugaba Jonathan ya kaddamar da Kamfe

Shugaba Jonathan Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu nazari na ganin shugaba Jonathan ne ake saran zai lashe zaben

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya kaddamar da kamfe dinsa na yakin neman shugaban kasa, gabanin zabukan da za a yi a watan Afirilu.

Shugaba Goodluck ya halarci wani gangami da jam'iyyar PDP mai mulkin kasar ta shirya a filin wasa na Lafiya a jahar Nasarawa da ke Tsakiyar kasar.

Dubban magoya bayan jam'iyyar PDP mai mulki sun ta kade-kade da raye-raye domin yin maraba da shugaban, da kuma mika sako na musamman ga masu adawa da shi.

Shugaba Jonathan ne ake saran zai lashe zaben na 9 ga watan Afrilu, sai dai yana fuskantar kalubale daga jam'iyyun hamayya.

A watan Janairu ne jam'iyyar PDP ta zabe shi a matsayin dan takararta, abinda ya saba tsarin karba-karba din da jam'iyyar ta amince da shi tsakanin Arewaci da Kudancin kasar.

Kuma wannan ne yasa masu lura da al'amura ke ganin addini da kabilanci zai yi tasiri a lokutan zaben.

Dukkan manyan 'yan takarar da ke adawa da shugaban dai sun fito ne daga yankin Arewacin kasar.

Jonathan ya gaji mulki ne daga marigayi Shugaba Umaru Yar'adua wanda ya rasu a zagayen mulkinsa na farko.