Dokar hana tusa a Malawi

Jami'ain shari'a biyu a kasar Malawi, suna gardama kan wata sabuwar doka da idan aka amince da ita a kasar za ta hana tusa cikin jama'a.

Ministan Shari'a George Chaponda ya ce sabuwar dokar za ta mayar da tusa a cikin jama'a cikin rukunin manyan laifuka.

"Duk wanda ke jin tusa ya nufi ban daki". In ji Ministan Shari'a.

Sai dai babban mai shigar da kara a kasar Anthony Kamanga ya ce dokar ba ta ambaci yin tusa ba. Ya ce dokar na nufin gurbata iska ne.

"Ai wannan akwai rashin tunani ace wai dokar za ta hana tusa, babu yadda za'a yi a hana tusa a cikin jama'a".

Ya ce dokar da ake magana a kai ta dade domin tun a shekarar 1929 ne aka kirkiro ta.

A wannan makon ne dai za'a kaddamar da dokar wadda ta bayana cewa; " Duk wanda ya gurbata iskar da ake shaka ya karya dokar kasar.

Mista Chaponda, wani kwararen lauya ya ce dokar ta hada da tusa a cikin jama'a.

"Za ku ji dadi idan ana tusa cikin jama'a?" In ji Chaponda a hirarsa da wani gidan rediyo.

Ya ce hakimai da shugabanni al'umma ne za su hukunta wadanda aka samu da laifin karya dokar.