Me ake ciki kan kawancen PNDS da MODEN?

A Jamhuriyar Nijar wasu 'yan kasar sun fara tofa albarkacin bakinsu a game da wasu rahotanni dake cewa akwai alamun an kulla wani sabon kawance tsakanin dan takarar jam'iyyar PNDS TARAYYA, Alhaji Mahammadou Issofou, da na jam'iyyar MODEN -LUMANA, Malam Hama Amadou, bayan zagayen farko na zaben shugaban kasar da aka gudanar a makon jiya.

Wannan zance dai ya soma karfi ne bayan kulla wani kawancen da Malam HAMA AMADOU din ya yi kwanakin baya, da wasu 'yan takara biyar mai lakabin ARN, hadin kan kasa.

A zagayen farko na zaben, Malam Mahammadou Issoufou ne ya zo na daya, Hamma Amadou kuma yana matsayi na uku.

Tun farko wasu jama'a da dama suna daukar kawancen na ARN tamkar wata hanyar taka ma dan takarar PNDS Tarayya, Mahammadou Issoufou birki .