Albashir zai amince da zaben rabagardama

Shugaban Sudan, Omar al-Bashir Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Sudan, Omar al-Bashir

Shugaban Sudan, Omar al Bashir, ya ce zai amince da sakamakon kuri'ar raba gardamar da aka gudanar yankin kudancin kasar.

Nan da 'yan sa'o'i ake sa ran samun sakamakon karshen, wanda ake jin zai tabbatar cewa, kusan kashi tasa'in da tara cikin dari na 'yan kudancin Sudan din, suna son ballewa.

Kuri'ar raba-gardamar ta biyo bayan yarjajeniyar kawo zaman lafiyar da aka kulla shekara ta dubu biyu da biyar, wadda ta kawo karshen yakin basasar da aka kwashe shekaru ashirin da daya ana gwabzawa tsakanin kudanci da arewacin Sudan din.