Ba a daina zanga-zanga ba a Masar

Hakkin mallakar hoto Reuters

Dubban daruruwan Misrawa sun sake yin zanga-zanga a dandalin Tahrir da ke tsakiyar birnin Alkahira, suna neman sai shugaba Mubarak ya yi murabus.

Wakilin BBC a wurin ya ce wannan ce zanga-zanga mafi girma da aka gani zuwa yanzu.

Tuni dama dai dandalin ya cika, sai kuma ga dubbai suna ta kwararawa zuwa can daga hanyoyin shigarsa.

Daya daga cikin wadanda ke zanga-zangar, mai wa'azin Islama, Safwat Hegazi, ya ce sauyi suke son kawowa a tsarin siyasar kasar.