An kafa Kwamitin gyaran tsarin mulki a Masar

An kafa Kwamitin gyaran tsarin mulki a Masar
Image caption Duk da wannan matakai masu zanga-zanga na ci gaba da neman shugaban ya sauka

Shugaban kasar Masar Hosni Mubarak ya fitar da wata doka da za ta bayar da damar kafa wani kwamiti da zai samar da sauye-sauyen da za a yiwa kudin tsarin mulkin kasar.

Ana saran gudanar da sauye-sauyen tsarin mulkin ne dai kafin zaben kasar mai suwa wanda za a yi a watan Satumban bana.

Lokacin da yake bayar da sanarwa a gidan talabijin, mataimakin shugaban kasar Omar Sulaiman, ya ce shugaba Mubarak ya bayar da umarnin kafa wani kwamitin na daban wanda zai tabbatar da aiwatar da sauye-sauyen da aka bayar da shawara akai.

Gida talabijin na kasar yace kwamitin kawo sauye-sauye kan tsarin mulkin, na daga cikin al'amuran da aka amince da su a tattaunawar da aka yi da 'yan adawa.

Sai dai har yanzu ba a san ko suwa nene za su zauna a cikin wannan kwamiti ba.

A bangare guda kuma masu zanga-zanga sun shafe daren jiya a dandalin Tahrir domin tilastawa shugaban ya sauka daga kan karagar mulki ba tare da bata lokaci ba.

Sai dai shugaban ya nace cewa ba zai sauka ba sai wa'adinsa ya kare a watan Satumba.