Mu muka kai harin Moscow - Doku Umarov

Mu muka kai harin Moscow - Doku Umarov Hakkin mallakar hoto RTV
Image caption Filin saukar jiragen sama na Domodedovo shi ne yafi kowanne a Rasha

Daya daga cikin mutanen da aka fi nema ruwa a jallo a Rasha Doku Umarov, ya ce shi ne ya shirya mummunan harin bom din da aka kai a filin saukar jiragen sama na Moscow.

Harin kunar bakin waken da aka kai a filin jiragen saman na Domodedovo ranar 24 ga watan Janairu, ya yi sanadiyyar kashe mutane 36, yayin da ya jikkata 180.

A wani fefen vidiyo da aka wallafa a intanet, Mr Umarov ya ce harin wani martani ne na "cin kashin da Rasha ke yiwa jama'ar yankin Caucasus".

Ya kara da cewa za su ci gaba da kai makamancin wannan harin.

Ana yi wa Mr Umarov kallon jagoran kungiyar masu fafutuka na yankin Arewacin Caucasus. Kuma yana bayyana kansa a matsayin shugaban masarautar yankin.

Yana kuma cikin tsirarin 'yan tawayen yankin Checheniya da suka rage, bayan da ya taba rike mukamin minista a wani bangare na gwamnatin yankin daga 1996-99.

Babu mamaki a kalaman

A wani fefen bidiyon da aka wallafa a ranar Juma'ar da ta wuce, ya yi barazanar kaddamar da hare-hare a bana, amma bai ambaci harin na filin jirgin saman Moscow ba.

A baya ma, Doku Umarov ya dauki alhakin harin watan Maris na 2010, wanda ya kashe mutane 39 a tashar jiragen kasa ta Moscow.

Kuma shi ake zaton ya kitsa harin watan Nuwamban 2009, inda mutane 26 suka mutu a wani jirgin kasa da ke kan hanyar zuwa St Petersburg daga Moscow.

Bayanin Doku Umaro na cewa shi ya shirya harin na Domodedovo ba zai zo da mamaki ga jama'ar Rasha ba, a cewar wakilin BBC Steve Rosenberg da ke birnin Moscow.

An dade ana alaknta mayakin na yankin Checheniya da hare-hare makamantan wannan.

Amma alkawarinsa na cewa akwai daruruwan 'yan kunar bakin wake da ke shirin kai hari a kasar, zai kara tsoratar da jama'a a fadin kasar ta Rasha.