Lauyan Charles Taylor ya fice daga kotu

Charles Taylor
Image caption Tsohon shugaban Liberia Charles Taylor

Lauyan da ke kare tsohon shugaban Liberia, Charles Taylor, ya fice daga kotu a husace a karshen shari'ar aikata laifukan yaki da ake yi ma tsohon shugaban a birnin Hague.

Lauyan, Courtenay Griffiths, ya harzuka ne byan da mai shari'a ya ki karbar wasu takardu da aka gabatar a makare.

Tun asali dama Mr Taylor bai halarci zaman kotun ba.

Lauyan ya ce, "muna ganin ba zai dace gare mu mu shiga cikin gabatar da bayani na baka ba, bayan galibinku kun ki amincewa ku karbi abinda muka gabatar."

Ranar Juma'a ne ake sanya ran kawo karshen shari'ar da aka kwashe shekaru ukku ana yi.

Ana zargin Mr Taylor ne da laifin goyon bayan 'yan tawayen Saliyau a lokacin yakin basasar kasar na shekaru goma, inda aka kashe dubban mutane da kuma datse gabobin wasu dubban.