Tunisia ta nemi sojojinta da suka yi ritaya su dawo bakin aiki

Tashin hankali a Tunisia Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ma'aikatar tsaron kasar Tunisia ta nemi sojojin kasar da sukayi ritaya daga aiki dasu dawo bakin aiki.

Yayin da gwamnatin Tunisia ke kokarin tabbatar da tsaro bayan boren da kasar ta fuskanta, ma'aikatar tsaron kasar tayi kira ga sojan da suka yi ritaya ba da jimawa ba, su koma bakin aiki.

Koda a jiya litinin gungun wasu mutane sun kona wani ofishin 'yan sanda, kuma ana cigaba da fuskantar fashi da sace-sace a kasar.

'Yan siyasa dake cikin gwamnatin hadin gwiwar kasar dai sun ce, magoya bayan tsohon shugaban kasar ne ke kokarin wargaza kasar ta Tunisia.

Wata sanarwa da ma'aikatar tsaron kasar ta fitar tayi kira ga sojin ruwa dana sama dana kasa da sukai ritaya daga aiki dama matasa wadanda suka kammmala samun horon aikin soji dasu dawo bakin aiki.

Ana yiwa wannan mataki kallon wani yunkuri na sake dawo da doka da kuma oda a kasar, makonni uku bayan wani boren da 'yan kasar suka yi yayi awan gaba da Shugaba Zinel Abidine Bin Ali.

Ko a makon daya gabata ma sai da wani tashin hankalin sabo ya sake barkewa, abinda daya jefa ayar tambaya game da zaman lafiyar kasar.