Za'a a gurfanar da Berlusconi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Silvio Berlusconi

Masu gabatar da kara na Italiya sun tabbatar da cewar suna son gurfanar da Pirayim Ministan kasar Silvio Berlusconi a gaban shari'a saboda yin amfani da iko ba kan ka'ida ba da kuma yin lalata da wata karuwa mai kankancin shekaru.

Masu gabatar da karar sun shigar da bukatar su ne a Milan bayan wani dogon bincike game da rayuwar Pirayim Ministan.

Masu shigar da kara dai sun ce Mr Berlusconi zai fuskanci tuhuma ne kan laifuka guda biyu; na farko shi ne yadda ya baiwa wata yarinya mai suna Ruby, 'yar shekaru 17 kudi, inda ya yi lalata da ita.

Laifi na biyu shi ne yin amfani da mukaminsa, inda ya kira 'yansanda domin sakinta, bayan an kama ta da laifin sata.

Shi dai Mr Bercusconi ya sha musanta wadannnan zarge-zarge.

A yayin da yake jawabi ga manema labarai, ya ce bita-da-kulli masu shigar da karar ke son yi masa, kuma hakan zai bata sunan kasar a idon duniya.

"Abin da masu shigar da kara ke son yi ya sabawa doka, da kuma majalisar kasa, domin kuwa basu da 'yancin gabatar da wannan batu. Babu wani abun ba dai-dai ba da aka aikata ."

'Yan kasar dai sun bayyana ra'ayoyinsu kan batun:

"Ya kamata a dauki mataki kan wannan batu, domin mu sani ko zargin da ake yi masa gaskiya ko kuwa a'a." In ji wani dan kasar.

Ita ma wata 'yar kasar cewa ta yi: "Dole ne ya yi murabus, ya kamata ya sauka, ko kuma kotu ta yi masa hukunci, kana ta ci tararsa, domin kuwa ba zamu rika zura ido kan irin wannan ta'asa ba."

A yanzu dai, an mika takardun tuhumar da ake yi masa zuwa wata alkalin Kotu dake birnin Milan, kuma za ta yanke hukunci kan batun cikin kwanaki kadan masu zuwa.

Idan dai aka sami Mr Berlusconi da laifin, to zai iya fuskantar zaman jarun na tsawon shekaru 17.