INEC ta maida martani game da korafe korafen 'yan takara

Shugaban hukumar zaben Najeriya Farfesa Attahiru Jega
Image caption Hukumar zaben Najeriya tace jerin sunayen 'yan takarar data fitar, sakamakon zabubbukan fidda gwanayen da jam'iyyun kasar suka gudanar ne

Hukumar zaben Nigeria mai zaman kanta, INEC ta maida martani ga cece-kucen da fitar da jerin sunnayen 'yan takarar da hukumar ta yi ke haifarwa a wasu sassan kasar.

Hukumar zaben dai tace sunayen da ta fitar sune na wadanda suka cancanta su yi takara a zaben mai zuwa, kuma duk wanda yake da wani korafi dangane da hakan, to kofar kotu a bude take.

Mataimakin kakakin hukumar zaben Najeriyar Nick Dazang ya shaidawa BBC cewar sai da hukumar ta tura wasu jami'anta domin su sa ido akan yadda aka gudanar da zabubbukan fidda gwanayen kafin ta kaiga wallafa jerin sunayen 'yan takarar da sukai nasara.

Ya kara da cewa dalilin wallafa sunayen tunda farko shine domin a tabbatar da cewar ainihin wadanda suka ci zaben fidda gwanayen da aka gudanar a baya, sune wadanda aka fitar da sunayensu, sa'annan kuma domin a tabbatar da cewar ba'a tsaida 'yan takara azzalumai ba

Jerin sunayen da hukumar zaben ta fitar dai ya janyo zafafen kalamai daga wasu 'yan takara, da jam'iyyun siyasa, inda har ma wasu jam'iyyun suka zargi hukumar zaben da sauya masu 'yan takara, abunda suka ce INEC din ba ta da hurumin yi.