An gudanar da zanga-zanga a jihar Nassarawa

A Najeriya rahotanni daga jihar Nassarawa dake yankin tsakiyar kasar, na cewa magoya bayan dan takarar gwamna na jam'iyyar CPC, Alhaji Tanko al-Makura sun gudanar da wata zanga-zanga, saboda kame dan takarar da 'yan sanda su ka yi a jiya.

Sai dai rahotanni na nuni da cewa 'yan sanda sun sake shi a yammacin ranar laraba, amma har yanzu ana rike da wasu daga cikin magoya bayanshi.

Masu zanga zangar dai sun kona tayoyi tare da datse tituna domin nuna rashin amincewarsu da tsarewar da 'yan sandan kasar ke da yiwa dan takarar na su.

Lamarin dai ya sa al'amura sun tsaya cik a garin Lafiya babban birnin jihar, yayin da 'yan sanda suka yi harbi a sama da kuma amfani barkonan tsohuwa domin tarwatsa masu zanga-zanagar.

An dai tsare Alhaji Tanko Al Makura ne bayan da wasu suka jefi tawagar yakin neman zaben Shugaba Goodluck Jonathan ranar litinin a birnin na Lafiya.

Rahotannin sun ce matasan sun fita kan titunan da safiyar ranar laraba ne abinda kuma yasa su yin arangama da jami'an tsaro.