Hosni Mubarak na wurin shakatawar Sharm El-Sheik

Hakkin mallakar hoto elvis

A halin yanzu dai Shugaba Hosni Mubarak yana fadarsa dake wurin shakatawa na Sharm el-Sheikh a kusa da tekun Bahar Maliya.

Babu wani cikakken bayani na ko zai ci gaba da kasance a can ne.

Sakatare Janar na kungiyar kasashen Larabawa Amr Moussa, wanda shi ma dan kasar Masar ne, ya ce murabus din da Mr Mubarak yayi, wata dama ce ta sake samar da fahimtar juna tsakanin 'yan kasa, tare da samarwa kasar makomar dimokradiyya.

Inda ya kara da cewa wannan lokaci ne mai tarihi ga kasar Masar, da alummar kasar da ma kasashen Larabawa baki daya.

Mataki ne da ba a yi tsammani ba, juyin juya hali ne da ba a yi tunanin aukuwarsa ba, kuma hadin kan 'yan kasa ne da ya samar da wani yanayi na daban a kasar Masar.