Tasirin yanar gizo da wayar salula a Masar

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Amafani da fasahar sadarwa ta yanar gizo ta taka muhimmiyar rawa wajen saukar shugaba Hosni Mubarak daga kan mulkin Kasar Masar.

Masana sun bayyana cewa wayar salula ta taka mahimmiyar rawa wajen sadarwa da kimanin kashi sittin da biyar zuwa saba'in cikin dari a bazuwar zanga- zangar a duk fadin kasar, musamman ma bayan da gwamnati ta toshe damar shiga shafukan yanar gizo.

Sun yi misali da cewa mafi yawan hotunan da aka nada, an yi amfani ne da wayar salula wajen daukar su, inda daga bisani aka saka shi a shafukan yanar gizo domin duniya ta gani.

Masu zanga-zanga sun yi amfani da kafofin yada labarai na zamani da suka hada da dandalin sada zumunta na Facebook da Twitter domin yada manufarsu.