India da Pakistan za su fara tattaunawa

India da Pakistan za su fara tattaunawa Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption India ce ta dakatar da tattaunawar bayan hare-haren da aka kai garin Mumbai

Kasashen India da Pakistan sunce sun amince su soma tattaunawa a kan dukkanin batutuwan da suka shafe su.

Hakan dai na nuni da komewa ga tattaunawar zaman lafiyarsu, wadda aka dakatar bayan hare-haren da aka kai a Mumbai cikin shekara ta dubu 2008.

A cikin wata sanarwar hadin guiwa, makwabtan biyu masu makaman Nukiliya sunce Ministan harkokin wajen Pakistan zai ziyarci India nan da watan Yuli domin sake duba ci gaban da aka samu a kan sasantawar.

Kafin wannan ziyarar, manyan jami'an gwamnatocin biyu za su gana domin tattauna batun yaki da ta'addaci da kuma makomar Kashmir - wato yankin nan da ke cikin tsaunukan Himalayas a kan iyakar kasashen da kowacce a cikinsu ke ikirarin na ta, wanda shi ne tushen rikicin da ke tsakaninsu.

Wakilin BBC Mark Dummet ya ce wannan dai tamkar dawo da tattaunawar sulhu ne tsakanin kasashen ba tare da bayyana hakan ba.

India ce ta dakatar da waccen tattaunawar bayan hare-haren da aka kai garin Mumbai, wanda ta zargi masu tada kayar baya a Pakistan da kai wa.