INEC ta yi rajistar fiye da mutane miliyan sittin

A Najeriya, hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta ce, ta yi rajistar masu zabe fiye da miliyan sittin da uku, wadanda ake sa ran za su kada kuria a babban zaben kasar da za'a yi a watan Afrilu.

Aikin rajistar, wanda ya dauki tsawon makonni uku, ya fara ne da tafiyar hawainiya, inda wasu rahotannin suka nuna cewa naurorin da ake aikin rajistar suna da matsala, yayin da wasu wuraren da ake rajistar aka rufe su.

Koda yake daga bisani, mahukunta sun bayyana cewa, sun shawo kan dukkanin wadannan matsaloli.

Bukatar sabunta rajistar dai ta biyo bayan gano cewar tsohon kundin rajistar wanda aka yi amfani da shi a shekara 2007 na cike da sunayen masu zabe na bogi.