Obama ya yaba da matakin sojin Masar

Hakkin mallakar hoto AFP

Shugaba Obama ya ci gaba da ganawa da wasu shugabannin kasashen duniya game da lamarin dake faruwa a Masar.

A jawabinsa na baya baya, Shugaba Obama ya yi maraba da jawabin da sojin Masar suka bayyana na tabbatar da mika mulki ga farar hula, domin tabbatar da demokradiyya a kasar.

Ya dai bayyana cewa wanzar da demokradiyya a Masar zai taimaka wajen samun daidaito a yankin gabas ta tsakiya.

Ya gana da Prime Ministan Birtaniya David Cameron ta waya, da takwaransa na Turkiyya Tayyib Erdogan da kuma Sarki Abdullah na Jordon.

Sannan kuma Shugaba Obaman ya tura wani babban mai bashi shawar zuwa Jordon da Israela domin ganawa da shugabanninsu kan tabbatar da kawancen Amurka a yankin Gabas ta tsakiya.

Wannan kuma ya biyo bayan sanarwar da sojin Masar suka bayar na cewa zasu ci gaba da mutumta yarjejeniyar zaman lafiyar da suka cimma da Israela a shekarar 1979