Sudan na bukatar majalisar dinkin duniya ta yaba mata

Tutar Kudancin Sudan Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Gwamnatin Sudan tana son majalisar dinkin duniya ta biya ta, saboda cika alkwarain data dauka na samar da cikakken tsaro a lokacin zaben raba gardamar 'yan cin kan kudancin Sudan

Gwamnatin Sudan ta nemi majalisar dinkin duniya ta yaba ma ta, saboda ciki alkawarin da ta yi na amincewa da sakamakon zaben raba gardama akan 'yan cin yankin kudanci da kuma samar da tsaro a lokacin zaben raba gardamar da aka gudanar.

Yayin da yake jawabi ga kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya, jakadan Sudan din, Daffa-Alla Elhaj Ali Osman ya kuma yi kira ga majalisar dinkin duniya ta sauya matsayinta dangane da shugaba Omar al-Bashir.

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya dai tana tuhumar shugaban Sudan, Omar al-Bashir da aikata laifukan yaki a yankin Darfur dake yammacin Sudan din.

To sai dai a wata sanarwar daya fitar a kwanakin baya, kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya soki yadda gwamnatin Khartoum din tayi aman wuta a yankin Darfur, yana mai cewar akwai bukatar a yiwa al'ummar yankin adalci