Tsuke bakin aljihu ya shafi Hukumar leken asirin Amurka

Darektan hukumar leken asiri na Amurka James Clapper, ya ce hukumarsa na fuskantar raguwar kudaden da ake ware mata.

Mista clapper ya bayyana cewa hakan na faruwa ne duk da barazanar dake karuwa ga harkar tsaron Amurka.

Darektan ya shaida wa wani kwamiti a majalisar dokokin kasar cewa, shi da sauran abokan aikinsa sun fahimci irin bukatar da ke akwai ta tsuke bakin aljihun gwamnati.

To amma ya kara da yin bayani game da jerin barazanar tsaro da kasar ke fuskanta daga aiyyukan kungiyar Al Qa'eda a kasashen Yemen da Somalia, da kuma irin hare haren da kasar ke fuskanta ta hanyar sadarwa ta Internet.