Gwamnatin Afirka ta Kudu zata kirkiro ayyukan yi

Jacob Zuma
Image caption Jacob Zuma

Shugaban Afrika ta Kudu, Jacob Zuma, ya ce gwamnatinsa zata kafa wani asusu na dala biliyan daya da miliyan dari biyu, domin kirkiro ayyukan yi, a kasar da sama da mutum guda cikin mutane biyar ba su da aikin yi.

A jawabinsa na shekara shekara ga al'umma kan halin da kasar take ciki, Mr Zuma yayi kira ga kampanoni masu zaman kansu, da su yi aiki tare da gwamnati, domin kirkiro ayyukan yi.

Mr Zuma ya kuma ce tsohon shugaban kasar, Nelson Mandela, ya na ci gaba da samun kyakkyawar kulawa, bayan rashin lafiyar da yayi fama da ita, mai nasaba da numfashi, wadda ta kai shi kwanciya a asibiti.