INEC ta janye Muhammad Abacha daga takarar Kano

Hukumar zabe a Najeriya, INEC, ta janye sunan Muhammad Abacha na jami'yyar CPC daga jerin 'yan takarar gwamnan jihar Kano.

Daraktan sashen sharia na hukumar, Alhaji Ibrahim Bawa ya ce hakan ya biyo bayan korafin da jam'iyyar ta yi cewa ba shi ne dan takararta a jihar ba.

Sai dai ya ce hukumar ta karbi kukan da Muhammad Abacha ya aika mata cewa shi ya yi nasara a zaben kuma jami'anta da su ka sa ido kan zaben fidda gwani na jam'iyyar sun tabbatar da shi ya yi nasarar.

Akan haka hukumar zaben ta rubutawa jam'iyyar takadar neman bahasin dalilinta na sauya sunansa da wani dan takara dabam.

Don haka kawo yanzu hukumar zaben ba ta tantance dan takarar gwamnan jihar Kano a jam'iyyar ta CPC ba har sai bayan jam'iyyar ta gamsar da ita.

Tuni dai Alhaji Muhammad Abacha ya kai karar jam'iyyar gaban kotu kuma hukumar zaben ta ce a shirye ta ke ta bi duk hukuncin da kotun ta yanke.