Ana ci gaba da matsawa Shugaba Mubarak lamba

Image caption Shugabannin sojan kasar ta Masar sun goyi bayan matakin da shugaba Mubarak ya dauka

Dubban 'yan kasar Masar sun fita kan titunan a birnin Alkahira, saboda sun fusata kan yadda shugaban kasar Hosni Mubarak, ya ki sanar da murabus dinsa, a jawabin da yayi ta gidan talabijin a daren Alhamis.

Dubban jama'a sun hallara a dandalin Tahrir, yayin da wasu dubban kuma suka kewaye gidan talabijin din kasar, da kuma fadar shugaban kasa mai cikakken tsaro:

Can ma a biranen Iskandariya da Suez wasu dubban masu zanga-zangar sun fito kan tituna.

Shugabannin sojan kasar ta Masar sun goyi bayan matakin da shugaba Mubarak ya dauka, na mika wasu ayyuka ga mataimakinsa.

Sojojin sun kuma yi alkawarin dage dokar ta baci da zarar yanayin da ake ciki ya kyautatu, da kuma bada tabbacin gudanar da sahihan zabubuka a kasar.

Martanin kasashen duniya

Kasashe na cigaba da nuna damuwa game da al'amuran da ke faruwa a kasar ta Masar.

Jamus ta ce, jawabin da shugaba Hosni Mubarak yayi a jiya, bai nuna samun ci gaban da aka zata ba, kuma ba zai kawo raguwar zaman dar-dar a kasar ba.

A nata bangaren, Burtaniya ta ce yanayin da ake ciki a Masar yana da hadari, kuma ta yi kira ga masu zanga-zangar da su nuna juriya.

Sakataren harkokin wajen Burtaniyar, William Hague, ya ce, abinda muke so kawai shi ne: "Su warware sabanin da ke tsakaninsu ta hanyar lumana da dimokradiyya".

Tun farko kuma, shugaban Amurka Barack Obama, ya ce matakan da gwamnatin Masar ta dauka ba su wadatar ba.

Yayin da can a Iran, shugaba Mahmoud Ahmadinejad ya bayyana zanga-zangar da ake yi a Masar din da cewa, "kamar wata farkawa ce daga barci".

Ya kuma ce nan ba da jimawa ba yankin Gabas ta Tsakiya zai rabu da Amurka da kuma Isra'ila.

Karin bayani