Zanga-Zangar Dimokradiyya a Algeria

'Yan sandan Algeria
Image caption 'Yan sandan Algeria

An tura 'yan sandan kwantar da tarzoma sama da dubu ashirin zuwa Algiers, babban birnin Algeria, yayinda masu zanga zanga ke hallara domin wani gangamin neman kafa tsarin dimokradiyya.

Gida talabijin na kasar ya ce masu zanga zangar ba su wuce su dari biyu da hamsin ba, yayinda wakilin BBBC a Algiers ke cewa dubban mutane ne suka yi cincirindo a babban dandalin birnin.

Da dama suna rera wakokin la'antar gwamnati, tare da neman a kyautata masu yanayin rayuwa, da kara samun walwala.

Kungiyoyin kare hakkin jama'a sun ce an kama mutane da dama.