Al'amura na daidaita bayan saukar shugaban Masar

Misrawa na murna Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Misrawa na murna

Bayan shafe sama da makonni biyu ana rikicin siyasa a kasar Masar, wanda ya kai ga saukar shugaba Hosni Mubarak a jiya, al'amurra sun fara komawa yadda aka saba.

Mutane a Dandalin Tahrir a birnin Alkahira sun fara wani gagarumin aikin share datti, bayan da aka kashe daren jiya an shagulgulan murna.

Har yanzu dai akwai wasu masu zanga zangar da suka rage, suna cewa zasu ci gaba da zama, har sai sojoji sun mika mulki ga farar hula. Obama zai tura wakili

Shugaba Obama kuma zai tura babban mashawarcinsa kan ayyukan soji zuwa Jordan da Isra'ila domin tattaunawa kan tasirin rikicin kasar Masar da kawayenta.

Wani jami'i ya ce, Admiral mike Mullen zai tattauna kan batutuwan da suka shafi tsaro, tare da kara bada tabbacin goyon bayan Amurka ga abokan burminta.

Zai gana da Sarki Abdullah na Jordan da kuma praministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.

Tun da farko Mr Obama ya ce ya zama wajibi majalisar koli ta mulkin sojan kasar Masar, wadda yanzu ke iko da kasar, ta tabbatar da an yi zabe na gaskiya da adalci.