'Yan sandan Ghana sun harbi 'yan gudun hijira

John Atta Mills, Shugaban Ghana
Image caption John Atta Mills, Shugaban Ghana

Rahotanni daga Ghana na cewa 'yan sanda sun bude wuta kan wasu 'yan gudun hijirar Liberia dake zaune a wasu sansanoni masu nisan kilomita 45 a yamma da Accra, babban birnin kasar.

Har yanzu babu cikakkun bayanai kan ainihin abin da ya faru, amma ana cewa an kashe 'yan kasar ta Liberia su uku, bayan da 'yan sanda suka yi harbi cikin jama'a, lokacin wata takaddama game da shugabancin sansanonin.

'Yan sandan sun kuma kama wasu daga cikin 'yan gudun hijirar.

Mutane dubu 13 ne ke zaune a sansanonin.