CFDR na goyon bayan PNDS a Zaben Nijar

A Jamhuriyar Nijar, wasu daga cikin jam'iyyun da ke cikin kawancen CFDR wadanda suka yi gwagwarmaya da yunkurin tazarce na tsohon shugaba Tanja Mammadu sun kara jaddada goyan bayansu ga dan takarar Jam'iyyar PNDS, Alhaji Muhammadu Issoufou, suna masu cewar zasu goya masa baya a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da za a yi a watan gobe.

Kawancen na CFDR ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai a yau.

To sai dai Jam'iyyar CDS Rahama, daya daga cikin jam'iyyun da aka kulla kawancen na CFDR da su, ba ta halarci wannan taro ba.

Cikin wata hira da Alhaji Dudu Rahama, daya daga cikin shugabanninta, ya ce talakawan jam'iyyar dai sun nuna masu cewa suna son ganin an ci gaba da kawancen ARN, dai zai mara baya ga Seyni Oumarou, dan takarar jam'iyyar MNSD Nasara, a zagaye na biyu na zaben.