Sojoji sun hana zanga zanga a dandalin Tahrir

Hakkin mallakar hoto AP

Masu zanga zanga na karshe da suka rage a dandalin Tahrir na birnin Alkhaira a kasar Masar, sun ce sojoji sun shaida musu cewar su kwashe ya-na-su ya-na-su su fice daga dandalin, idan ba haka kuwa za su kakkamesu.

Wannan al'amari dai ya zo ne kwana daya kacal bayan da sojojin da ke jan ragamar mulkin kasar suka jingine tsarin mulkin kasar sannan suka rusa majalissar dokoki.

To saidai sabanin umarnin na sojojin, masu zanga zangar na ci gaba da tururuwa zuwa dandalin na Tahrir, yayin da ma'aiakata da dama ke ci gaba da yajin aiki.

Tunda farko dai a safiyar yau ne, sojoji suka shiga dandalin Tahrir, domin kawar da sauran masu zanga-zangar da suka rage.

A cikin 'yan awannin da suka gabata, sojojin sun yi ta rarrashin masu zanga-zangar kan su bar dandalin, inda suke ture su, kuma wani lokacin har kama su su ke yi.

Sojoji na ta kwashe bargunan da masu zanga-zangar su ke yin amfani da su, inda suke zuba su a wasu motoci da aka kawo wajen.

Sai dai a yayin da zanga-zangar ke zuwa karshe, an fara yajin aiki a wasu sassan kasar.

Ma'aikatan da suka hada da na bankuna, da masu sufuri, da ma 'yan sanda, sun yi tattaki zuwa ma'aikatar harkokin gida ta kasar.

Da wuya dai a iya magance irin wannan yunkuri da 'yan kasar ta Masar ke yi, kasance sun kwashe shekaru da dama cikin kuncin rayuwa.