Gwamnatin Iran ta tsare Shugaban 'yan adawa Mousavi

'Yan sanda a Iran sun yi wa shugaban 'yan adawa Hossein Mousavi daurin talala a gidansa.

Rahotanni da aka wallafa a shafin shugaban 'yan adawan na nuni da cewa an tsare shi domin hana shi halartar wani gangami a birnin Tehran domin nuna goyon baya ga sauyin da aka samu a Masar.

Tsare shugaban 'yan adawan na daya daga cikin tsare wasu 'yan adawa a kasar ciki har da Mehdi Karroubi, wanda shi ma aka yiwa daurin talala.

Kungiyoyin 'yan adawa da dama sun sha alwashin gudanar da zanga-zanga, abinda kuma mahukunta a kasar su ka haramta yi.

Munafar siyasa

Duk da cewa dai Mahukunta a Iran sun goyi bayan zanga-zangar da aka yi a Masar, sun ce wanda 'yan adawa za su gudanar a kasar na da manufar siyasa.

Gwamnatin kasar ta tsaurara matakan tsaro a babban birnin kasar, kuma an toshe hanyoyin sadarwa na Intanent da kuma na kafofin yada labarai na tauraron dan adam.

Image caption Hossein Mousavi

Masu sharhi dai na nuni da cewa gwamnatin Iran na kokarin hana 'yan adawa taro ne kada jama'ar kasar su yi koyi da abinda ya faru a Masar.

An dai gudanar da zanga-zanga a kasar ne a shekarar 2009 bayan takkadamar da ta biyo bayan zaben Shugaba Mahmoud Ahmadinejad a karo na biyu.

Wani abin mamaki kuma shi ne, yadda wani mutum ya hau tsanin wata motar ginin mai tsawo inda yake gayyatar mutane da su fito zanga zanga, In ji Wakilin BBC Mohsen Asgari a birnin Tehran.

Mutumin ya yi barazanar hallaka kansa idan jami'an tsaro suka matso kusa da shi, amma daga baya dai 'yan sanda sun cafke shi.

Har wa yau dai a safiyar ranar Litinin, motocin 'yan sanda a kasar sun toshe hanyar zuwa gidan Mista Mousavi da motocinsu, kuma sun katse wayoyinsa.

A makon daya gabata ma, an tsare magoya bayan Mista Mousavi da dama a kasar.